Da Dumi-Dumi: Kwamishinar Muhallin Jihar Gombe Ta Ajiye Aiki

Rahotanni dake shigo mana yanzu daga Jihar Gombe na bayyana cewar Kwamishinar muhalli ta Jihar Dr. Hussaina Goje ta ajiye mu?aminta na Kwamishinan muhalli da kula gandun daji.

Rahotanni sun bayyana cewar Kwamishinar ta ajiye aikinta ne saboda wasu dalilai, na ra?in kanta wa?anda ba a bayyana ba.

Sai dai jama’a na danganta ajiye mu?amin nata da hatsaniyar siyasar da aka samu ranar juma’a a Gombe tsakanin magoya bayan gwamnatin jihar da magoya bayan mahaifinta wato Sanata Danjuma Goje.

Indai jama’a ba su manta ba a jiya juma’a tarzoma ta barke tsakanin magoya bayan tsohon Gwamnan Jihar kuma Sanata mai ci ?anjuma Goje da matasa masu goyon bayan gwamnatin jihar, lamarin da ya haifar da asarar rayuka.

Related posts

Leave a Comment