Mai magana da yawun shugaban ?asa, Garba Shehu, ya bayyana cewa “Shugaba Buharin yafi mafi yawan matasan da suke ?alubalantarsa a kan matsayin lafiyarsa, ?oshin lafiya”.
Garba Shehu ya fa?i hakan a ranar Alhamis, yayin wata hira da yayi a Channel TV, a tsarin allon gani – gaka na (zoom).
Buhari, yanzu haka ma yana Brussels da Belgium domin halattar taron ?oli na shida 6 na ?ungiyar ha?aka ta tarayyar Turai da Africa (EU-AU).
” shugaban ?asa garau yake. Mu a gurinmu, abin burgewa shi ne, mutane sun fara jin da?in cewa shugaban ?asa yana cikin ?oshin lafiya, kamar yadda wasu daga hotunan nan suka nuna”.
”Mun sha fa?a cewa, shugaban yafi da yawa daga cikin matasan da suke ?alubalantar sa akan matsayin lafiyar sa, koshin lafiya. Hakan ko ya bayyana karara daga abin da ya fito daga ?asar Belgium”. Inji Garba Shehu
Tunda ya kama aiki, shugaba Buharin yake jele zuwa kasar Birtaniya, akan matsayin lafiyar sa ; lamarin da ya janyo Sanya alamomin tambaya akan koshin lafiyar shugaban.
A wani rahoto da jaridar The Cable suka wallafa, a shekarar 2021, an gano cewa Buhari ya shafe kimanin kwanaki ?ari da saba’in 170 a ?asar Birtaniya yana fafutukar lafiyarsa, tun bayan shigarsa Ofis.
