Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gabanin ?addamar da majalisar dokoki ta 10 a watan Yuni, fusatattun za?a??un sanatoci daga APC sun gana da mambobin kwamitin gudanarwar jam’iyyar mai mulkin Najeriya a hedkwatarta da ke Abuja.
Daga cikin sanatocin da suka halarci taron, akwai Abdulaziz Yari da Orji Kalu da Mohammed Musa da kuma Sadiq Umar.
Shugaban APC, Sanata Abdullahi Adamu da Sakataren jam’iyyar na ?asa, Iyiola Omisore da shugabar mata ta APC Beta Edu, su ma sun halarci taron.
Da yake jawabi ga kwamitin, Orji Kalu wanda ke neman takarar shugaban majalisar dattawa ya ce bai wa kowanne ?angaren Najeriya dama abu ne mai kyau.
Ya ?ara da cewa, bai kamata jam’iyyar ta mi?a shugabancin majalisar da ba a kai ga ?addamar da ita ba, bisa dalilai na yawan ?uri’un da kowanne yanki ya bayar wajen samun nasarar za?a??en shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ba.
A cewarsa, shiyyar da ?uri’unta ba su taka kara sun karya ba a za?en da ya gabata, na iya samar da ?uri’u masu yawa ga jam’iyyar a za?uka masu zuwa.
Shi ma Yari, wanda ya gabatar da takardar adawa da za?a??un sanatocin suka rubuta ga Shugaban APC, ya nemi jam’iyyar ta sake nazari kan tsarin da ta amince da shi saboda adalci da daidaito.
A ranar Litinin ne kwamitin gudanarwar APC ya raba mu?aman shugabannin majalisar tarayya ta goma.
APC ta mi?a shugabancin majalisar dattawa ga Sanata Godswill Akpabio (shiyyar kudu maso kudu) sai mu?amin mataimakin shugaban majalisar ga Sanata Barau Jibrin (shiyyar arewa maso yamma).
Sai kuma mu?amin kakakin majalisar wakilai ga Abass Tajudeen (Arewa maso Yamma), mu?amin mataimakin kakakin ga Ben Kalu (yankin Kudu maso gabas).
