Hakan na kunshe ne cikin rahoton da hukumar tattara bayanan sirri kan sha’anin ku?i a ?asar (NFIU) ta fitar a ranar Talata.
Ta ce wa?anda ake zargi da taimakawa ta’addancin sun kunshi mutum tara da kuma masu kamfanonin canji.
Rahoton na NFIU ya nuna cewa kwamitin sa ido kan takunkumi a Najeriya ta zauna ranar 18 ga watan Maris, inda aka bayar da shawarar saka takunkumi kan wasu mutane da kuma kamfanoni saboda hannu a tallafawa ta’addanci.
“Babban Attoni Janar na ?asa, tare da amincewar shugaban ?asa, ta ayyana wa?annan mutane da kamfanoni don a saka su a jerin wa?anda aka saka wa takunkumi,” kamar yadda raoton ya bayyana.
Cikin jerin mutanen har da Tukur Mamu, wanda ake ci gaba da shari’arsa kan zargin taimakawa ?an bindiga wa?anda suka kai hari kan jirgin ?asan Abuja-Kaduna a watan Maris ?in 2022.
A cewar kundin da NFIU ta fitar, ta ce Mamu ya tallafawa ta’addanci ta hanyar kar?ar ku?i da ya kai $200,000 daga hannun wa?anda aka yi garkuwa da ?an uwansu da kai wa masu garkuwa, don sakin fasinjojin jirgin ?asan na Abuja-Kaduna.
Har ila yau, rahoton ya ce ?aya daga cikin mutanen da ake zargi shi ne wanda ya kai hari kan cocin Katalika na St. Francis da ke Owo, a jihar Ondo ranar 5 ga watan Yulin, 2022.
An bayyana ?aya daga cikin mutane a matsayin mamban ?ungiyar Ansarul Ansarul Muslimina Fi Biladissudam, wadda ke ala?a da Al-Qaeda da ke yankin Maghreb.
Akwai kuma wani babban kwamandan ?ungiyar ISIS a Afrika ta Yamma, wanda shi ma ake zargi da taimakawa ta’addanci a Najeriya.
