Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ayyana aikin ‘yan bindiga a matsayin aikin ta’addanci a hukumance, kamar yadda FIJ ta tattaro.
Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a Abubakar Malami ne ya bayyana hakan yayin da ya bayyana a shirin ‘Barka da Hantsi’ na gidan Talabijin na Najeriya (NTA) a ranar Talata.
Ya ce ofishinsa na aiki don duba hukuncin da kotu ta yanke wanda ya umarci gwamnati ta ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda.
A ranar Laraba babbar Kotun Tarayya ta samu takardar, inda Malami ya sanya hannu a cikinsu.
Mai shari’a Taiwo Taiwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya amince da bukatar da gwamnatin tarayya na neman alanta ‘yan bindiga da ‘yan fashin daji a matsayin ‘yan ta’adda.
