Gwamnatin Kano Ta Wanke Ado Doguwa Daga Zargin Kisan Kai

Ma’aikatar shari’a ta jihar Kano ta ce binciken da ta gudanar kan tuhumar da ake yi wa ?an majalisar wakilan tarayya, Alhassan Ado Doguwa kan laifin kisan, ya nuna cewa ba a same shi da laifin da ake zargi ba.

Lokacin da ya yi wa manema labarai bayani, kwamishinan shari’a na jihar Kano, Lawan Musa Abdullahi ya ce an samu sa?ani da dama cikin bayanan da aka samu daga wurin shaidu.

Ya ?ara da cewa a yayin da suke gudanar da bincike sun gano cewa ma’aikatan asibiti ba su yi cikakken bincike kan mutanen da ake zargin an harba da bindiga ba, soboda haka ba a iya tabbatar da cewa an harbe su ba.

Kwamishinan ya ce an gudanar da bincike kan bindigogi da harsashai da ke hannun ‘yan sandan da ke tare da ?an majalisar a lokacin da rikicin ya faru.

Sai dai a bayanin nasa babu wata shaida da ta nuna cewa an yi amfani da bindigogin, kasancewar jami’an ?an sandan sun mayar da daidai adadin harsasan da ke a hannunsu.

Related posts

Leave a Comment