Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a ranar Talata ce Majalisar Tarayya ta amince da saka tsarin tsaida ?an takarar da aka tsaida ta hanyar sulhu, a cikin ?udirin Dokar Za?e da yanzu haka aka yi wa kwaskwarima.
Da farko Majalisar Tarayya ta amince da za?en kai-tsaye da kuma za?en fidda-gwani ta hanyar wakilan jam’iyya kawai, banda fitar da gwani ta hanyar sulhu, ba tare da yin za?e ba.
Yanzu kenan majalisun biyu sun amince kowace jam’iyya ta bi hanyoyin guda uku wajen fidda ‘yan takarar ta daga za?en 2023.
Yayin da Majalisar Tarayya ta koma zama a ranar Talata, ta yi ke?antaccen zama, inda ?an Majalisa daga Jigawa, Abubakar Fulata ya gabatar da uzirin cewa su amince da ?udirin Doka na 82(b), wanda ya bada ?ofar jam’iyyar da ta ga dama za ta iya tsayar da ?an takara ko da ba a yi za?e ba, matsawar dai an cimma yarjejeniyar sulhun janye masa ne sauran ‘yan takara.
Hakan kuma aka yi, dukkan sauran mambobi suka amince da hakan.
A wani ?warya-?warya kuma ta?aitaccen cimma matsaya da Majalisar Dattawa ta yi a ranar Talata, ta sake yi wa ?udiri na 84 na Dokar Gyaran Za?e Kwaskwarima.
An yi kwaskwarima ?in ce ta yadda idan Shugaba Muhammadu Buhari ya sa mata hannu, za ta bai wa jam’iyyun siyasa damar kowace ta bi tsarin da ya fi daidai a gare ta wajen za?en fidda gwani.
A cikin ?udirin gyaran dokar za?en dai wanda Majalisar Dattawa ta sa wa hannu cikin 2021, sun rattaba cewa za?en fidda gwanin kowace jam’iyya zai kasance na ‘yar-tin?e ce.
Sai dai kuma Shugaba Muhammadu Buhari bai amince da wannan ?udirin ba.
Dalili kenan ya maida wa majalisa domin ta yi masa kwaskwarima.
Yayin da Majalisar Dattawa ta amince da za?en kai-tsaye ko ‘yar tin?e ko kuma tsayar da ?an takara a bisa tsarin yarjejeniyar amincewa, ita kuwa Majalisar Tarayya ba ta amince da fitar da dan takara ta hanyar cimma yarjejeniyar tsayar da mutum ?aya ba tare da za?e ba (wato consensus candidate).
Farkon makon jiya ne Majalisar Dattawa ta yi wa ?udirin Gyaran Dokar Za?e Kwaskwarima kamar yadda Shugaban Muhammadu Buhari ya nemi ta yi, kafin ya sa mata hannu
Gyare-gyaren Da Majalisar Dattawa Ta Yi Wa ?udirin Gyaran Dokar Za?e:
Majalisar ta fara yin gyaran gaggawa kan ?udiri na 87, wanda ya yi magana kan irin za?en fidda-gwanin ‘yan takara daga kowace jam’iyyar siyasa.
A yanzu an amince kowace jam’iyya ta za?i gwanayen ta bisa tsarin ‘yar tin?e, ?ato-bayan-?ato ko za?en game-gari.
Da farko dai Kudirin Gyaran Dokar Za?e ya amince a yi za?en kai-tsaye, ba na wakilan jam’iyya ba, wato ‘delegates’.
Wannan tsari ne ake kai a ?asar nan, wanda kuma ?o?arin kawar da shi a za?en 2023 bai yi nasara ba, biyo bayan fatali da tsarin za?en kai-tsaye da Buhari ya yi bisa dalilin cewa zai ci ma?udan ku?a?e wajen gudanarwa.
An amince da ?udiri na 84, wanda ya bada damar ko jam’iyya ta yi za?en kai-tsaye ko kuma tsarin wakilan jam’iyya, wato ‘delegets’.
An kuma amince da ?udiri na 84(2), wanda ya bada damar cewa jam’iyya za shirya za?en fidda gwani ta hanyar wakilai, ko kumà a cimma yarjejeniyar tsayar da wani ba tare da an yi za?e ba.
A za?en fidda-gwamnin ?an takarar shugaban ?asa, an gindaya cewa tilas sai an yi Taron Gangamin Jam’iyya a kowace jiha 36 da Abuja FCT, domin wakilan jam’iyya daga maza?u su yi za?en ‘yan takara.
Haka nan kuma ?udirin ya ce za a shirya babban za?e na ?asa, inda za a jaddada ?an takarar da ya fi sauran ‘yan takara yawan ?uri’u.
A labarin, Shugaban Kakakin Majalisar Dattawa Ahmad Lawan, ya bayyana ce Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya kowace za ta yi zaman yi wa ?udirin Gyaran Dokar Za?e Kwaskwarima a ranar Laraba, domin a cire wuraren da ake tankiya a kai, sannan su sake aika wa Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu.
Lawan ya yi wannan ?arin haske ne a ranar Talata da dare, yayin da ya ke ganawa da manema labarai, bayan ganawar da ya yi a ke?ance tare da Shugaba Muhammadu Buhari.
Lawan ya ce za su yi haka ne domin a samu damar sa wa sauran ?udirorin dokar hannu su zama doka, yadda za a gyara tsarin za?e a 2023.
Shugaban Muhammadu Buhari dai ya ?i sa wa ?udirin hannu saboda dalilan da ya kawo.
Bayan an yi ta ce-ce-ku-ce ne kuma sai Buhari ya ce zai iya sa wa ?udirorin hannu su zama doka, amma idan an cire wuraren da ake tankiya a ciki.
Lawan ya ce, “Idan Allah ya yarda a ranar Laraba, 18 Ga Janairu Majalisar Tarayya da Majalisar Dattawa kowace za ta yi zaman gyaran ?udirorin, ta yadda za a gaggauta aika wa Shugaban ?asa ya sa hannu.
“Aiki ne da za mu iya kammalawa a rana ?aya mu aika masa. Amma idan aikin ya wuce yau, to mu da aika masa sai farkon mako mai zuwa.
“Na san dai tabbas za su yi gyaran ne yadda za a ?yale kowace jam’iyya ta bi tsarin da ta ke son bi wajen za?en fidda gwani, wanda ke ?aya daga cikin wuraren da Buhari bai amince a yi za?en kai-tsaye, ‘yar-tin?e ko ?ato-bayan-?ato ba.
