Yayin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke ?o?arin mi?a mulki bayan shekara takwas, shin wane tasiri manufofinta suka yi kan harkar noma?
BBC ta tattauna da shugabannin wasu ?ungiyoyin manoma a Najeriyar wa?anda suka bayyana yadda harkar noma ta kasance a tsawon mulkin shugaban mai barin gado.
Akasarin manoman sun yaba wa gwamnatin ta shugaba Muhammadu Buhari, wa?anda suka ce harkar noma ta inganta ta hanyar taimaka masu tsayawa da ?afafunsu.
Manoman sun ce a cikin shekara takwas na gwamnatin Muhammadu Buhari, shugaban ya ?ullo da shirye-shirye wadanda suka amfanar da su tare da samar da wadataccen abinci da ake amfani da shi a ?asar.
?aya daga cikin matakan da Buhari ya ?auka shi ne gar?ame iyakokin ?asar ta ?asa inda aka hana shiga da shinkafa yar waje cikin Najeriya.
Shugaban ?ungiyar manoma ta NICAS, Sadiq Daware ya ce manoma sun ci gajiyar gwamnati da za ta tafi.
