Labarin dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewar Gwamnan Jihar Aminu Bello Masari ya yi fatali da maganar zaman sulhu da yan bindigan, wa?anda suka addabi jiharsa da sauran jihohin arewa ta yamma.
Masari ya bayyana matsayarsa ne yayin zantawa da kafar watsa labarai ta DW hausa, ranar Asabar.
Gwamnan ya maida martani ga wasikar dake yawo ta neman zaman sulhu, wanda gawurtaccen ?an bindiga Bello Turji, ya aike wa gwamnati.
Gwamna Masari, wanda a baya gwamnatinsa ta rungumi tattaunawar sulhu, yace ba sauran tattaunawar sulhu tsakaninsu da yan bindiga a yanzu sai kisa kawai.
Masari ya bayyana cewa abin da wasikar Turji ta ?unsa ba gaskiya bane. Gwamnan yace: “Sulhu da wa? Waye shi da yake neman sulhu ko a tsagaita wuta? Shi babban ma?aryaci ne, bai isa ya fa?a mana yadda za’a zauna lafiya ko sulhu ba.”
“?aje ka samu iyalan wa?anda yan bindiga suka kashe, ku nemi sulhu da su, kuga yadda zata kaya. Kuma har da saka wasu sharu??a, waye shi da zai kafa mana sharu??a?” “Shi ke neman sulhu amma har yana da bakin kafa wasu sharudda da za’a cika.”
Tawagar Turji na ?aya daga cikin kungiyoyin yan ta’adda da suka addabi yankin arewa maso yamma da wasu sassan arewa ta tsakiya.
