An bayyana cewar gwamnati mai ci a yanzu ta APC ta gaza ta kowane fanni a shugabanci, lamarin da ya zama dole a ?auki matakin canza ta.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin jigo a jam’iyyar PDP ta Jihar Kaduna mai neman jam’iyyar ta tsayar da shi takarar kujerar ?an majalisar tarayya a ?aramar hukumar Kaduna ta kudu Honorabul Hussaini Abdulkarim wanda aka fi sani da suna Kero, a yayin gabatar da aniyar takararshi a sakatariyar jam’iyar.
Hussaini Kero ya bayyana cewar da fari bai yi niyyar shiga takara ba amma biyo bayan nema da roko da aka yi mishi ya sa ya amsa kiran jama’a ya fito domin ba da tashi gudummuwar.
?an siyasar ya koka dangane da yadda APC ta gaza yin wani kata?us a al?awurran da ta yi, wanda hakan ya haifar da koma baya da matsi ga jama’a, inda ya sha alwashin kawo sauyi idan ya cimma nasara.
Daga karshe ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar da su kula su kuma tuna amanar dake kansu ka da su ci amanar jam’iyyar ta hanyar ?ora wa?anda ba su dace ba domin kwadayin abin duniya.
