Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Jirgin Kasa A Hanyar Abuja

Rahotanni sun ce wasu ?an bindiga sun tayar da bam a titin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna da ke ?auke da fasinja 970.

Rahotanni sun ce maharan sun yi nasarar hana jirgin tafiya, inda suka bu?e wuta.

?aya daga cikin fasinjan da ke cikin jirgin ya tabbatar wa da harin, inda ya ce maharan sun kwashi mutane sun tafi da su. Sannan jami’an tsaron da ke cikin jirgin sun yi musayar wuta da ?an bindigar.

Ya ce sun kashe mutum guda. “Mun ji ?arar harbe harbe, muna cikin tashin hankali,” in ji shi.

Wani ma’aikacin tashar jirgin a Rigasa ya shaida cewa “jirgin ya kamata ya iso misalin ?arfe 8:20 amma har yanzu ba labari.”

Hukumomin sufurin jiragen ?asa ta Najeriya da hukumomin gwamnatin Kaduna ba su tabbatar da al’amarin ba.

Related posts

Leave a Comment