Gombe: Hukumar Civil Defence Ta Yi Babban Kamu

A cigaba da dakile ayyukan ?ata gari a fa?in Jihar Gombe rundunar tsaro ta Civil Defence reshen jihar tayi nasarar tsare wani ?an shekaru 37 Ahmed Muhammad Kakamu da ake zargi cewa ya damfari wasu mutane 15 kudi har sama da naira miliyan 40.

Da yake magana da manema labaru Jim kadan bayan an nuna wanda ake zargin ga manema labaru, Waziri Baba Goni yace sun tsareshi biyo bayan korafi da mutanen suka kawo ga rundunar tasu.

Yana mai karawa da cewa ya cuci mutanen ne kudi har sama da naira miliyan 40. Kwamandan yaja hankalin ‘yan kasuwa da cewa a kullum su rinka kula da kuma sanin irin mutane da zasu rin?a yin hulda kasuwancin na makudan kudi dasu domin kaucewa fada wa hanun ‘yan damfara.

Muhammad Goje, Muhammad Bappah da Salmanu Muhammad sune wasu daga cikin wadanda aka cutar, sun kuma bayyana fatar cewa za a bi musu ha?kin su ayi musu adalci, suna masu shawartan ‘yan uwan su ‘yan kasuwa da cewa su kasance ko da yaushe masu kula.

Za a dai gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Related posts

Leave a Comment