Boko Haram Da ISWAP Sun Yi Sansani A Kaduna – Kwamishinan Tsaro

Rahoton dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnatin Jihar ta nuna damuwa game da ?aruwar ayyukan ‘yan bindiga masu i?irarin jihadi a jihar.

Kwamashinan Tsaro Samuel Aruwan ya shaida cewa wannan ne abin da ya fi damun su cikin rahoton tsaro da aka fitar na rubu’in farko na 2022.

Yace “?an ta’adda na ba wa mazauna yankunan jihar kyautuka” don jan hankalinsu shiga cikin ?ungiyoyin.

Gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana damuwa cewa “?an ta’adda” na komawa arewa maso yamma daga arewa maso gabas da zimmar tashin hankali.

Ya bayyana cewa babban za?en 2023 ka iya gamuwa da cikas idan har ba a ?auki mataki kan matsalar tsaro ba a jihar.

Related posts

Leave a Comment