Sanannen Lauyan nan mai rajin kare ha??in jama’a Femi Falana ya zargi Ministan Shari’a Abubakar Malami da yin kutse ga Babbar Kotun Tarayya ta yadda ta bayar da hukunci mai cike da tarna?i akan matsayar sashe na 84(12) na Sabuwar Dokar Za?e ta 2022.
Falana ya ce Malami ya yi biris, ya nuna kamar bai ma san akwai wani hukunci ko umarnin kotu wanda ya haramta masa yin katsalandan a kan dokar. Amma sai ya jajirce cewa shi sai ya yi amfani da umarnin Babbar Kotun Umuahia, wadda ta bayar da umarnin a soke wannan sashen gaba ?aya.
Falana wanda babban lauya ne (SAN), ya fitar da sanarwa inda ya bayar da cikakken bayanin yadda Manyan Kotunan Tarayya guda uku suka bayar da mabanbantan hukunce-hukunce. Daga nan Falana ya ?ora laifin gaba ?aya a kan Ministan Shari’a Malami.
“Don haka sai Falana ya ce ya kamata Malami ya sani cewa ba fa zai iya yin yadda ya ga dama ba, ta hanyar bin umarnin da ya ga dama, kuma ya bijire wa wadda ya gada dama.
“Sannan kuma babu sauran tantama, tabbas Ministan Shari’a ya damalmala hukuncin Babbar Kotun Tarayya har ta bayar da baddalallun hukunce-hukunce a kan sashe na 84(12) na Dokar Za?e ta 2022.” Inji Falana.
