Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar a kalla mutum sama da 40 ne ‘yan bindiga suka harbe a wani hari da suka kai a yankin ?aramar hukumar Giwa dake arewacin Jihar.
Rahotanni sun bayyana cewar Maharan sun kai hare-haren ne a garuruwa da ?auyuka daban-daban na ?aramar hukumar Giwan.
Wannan na zuwa ne bayan wani hari da ‘yan bindiga suka kai a filin jirgin sama na Kaduna a ranar Asabar ?in da ta wuce, inda suka kashe a ?alla ma’aikata biyu na filin jirgin.
A yanzu haka hare-haren da ake yawan kai wa jihohin Zamfara da Neja masu ma?wabtaka da Kadunan sun sa mutune barin garuruwansu.
Tunin aka yi jana’izar wa?anda aka kashe ?in a wasu garuruwan na yankin ?aramar hukumar amma har yanzu a wani garin ba a yi zana’izar mutanen da suka mutu ba.
Wani magidanci daga garin Tsaunin-Mayau da yanzu haka ke gudun hijira a wani garin bayan ya ?etare rijiya da baya ya yi ?arin bayani.
“Kashe mu suke yi kamar suna kashe kiyashi. Da ?arfe hudu na yamma suka dirar mana, a ?alla ba a ?asara ba sun zo da babur ya kai 300.
“Sun kashe mutum 14 nan take a gidana, gawarwakin ma suna nan ba a kwashe su ba, ba a yi jana’izarsu ba.
“Ba a yi jana’ziarsu ba don kowa ya gudu ana tsoron cewa za su dawo su sake kashe mutane, duk garin ya tarwatse.
“Tsakanin garuruwan nan uku akwai mutum sun fi dubu ?aya tsakanin mata da maza da yara. Hanyar cike take da ?an adam, suna nan kowa a ?afa yake tafiya.”
Wani zai yi mamaki ko ina jami’an tsaro suke a wannan lokacin?
Shaidan ya ce “wa yake maganar jami’an tsaro, kowa ta kansa yake. Ni kaina babur ya fi 50 da suka kewaye gidana.
“Haka suka fito da ni suka ce ina wayata? Na ?auka na ba su. Suka ce ina ku?i? Na ce ba ni da ku?i.
“Suka sake tambayata ina makami? Na ce musu ba ni da shi.
Haka suka yi ta min tambayoyi, da kamar za su harbe ni sai kuma Allah Ya taimake ni dai ba su harbe ni ba,” in ji shi.
Amma ya ce ya san Allah ne Ya ku?utar da shi ba wai don ya fi ?arfinsu ko dabararsa ba.
