Rahotanni daga birnin Kebbi na jihar Kebbi na bayyana cewar Ministan shari’a kuma Antoni Janar na ?asar nan, Abubakar Malami, ya bayyana shirinsa na neman takarar gwamnan Kebbi a babban za?en 2023 dake tafe.
An ruwaito cewa Malami, wanda ya bayyana shirinsa ranar Alhamis, 28 ga watan Afrilu, 2022, yace ya yanke shawarar takara ne bayan amsa kiran da mutane ke masa na ya zama gwamna.
Malami ya bayyana hakan a jawabin da yayi a Birnin Kebbi yayin tattaunawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC mai mulkin Jihar.
“Mutanen jihar ne suka matsa min in nemi gwamna a 2023. Bisa tarbiyyan gidanmu kuma ‘dan malamin addini, ba zan nemi wani mukami ba ko in ga kaina na cancanci wani matsayi sai idan al’umma sun bukata.”
“Na bada gudunmuwa mai yawa ga kasar nan da kuma jihar nan wajen samar da ayyukan yi, yaki da talauci, noma da taimakon mata.”
