Manchester United ta doke Arsenal da ci 3-1 a wasan mako na shida a gasar Premier League da suka buga ranar Lahadi a Old Trafford.
United ta fara cin kwallo a minti 35 ta hannun Anthony, sabon dan wasan da ta dauka a bana daga Ajax.
T?un a minti na 12 da fara tamaula Gabriel Martinelli ya ci Manchester United kwallo, amma aka soke ta cewar an yi wa Eriksen keta tun farko.
Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Bukayo Saka ya farke kwallon da aka ci Gunners.
Sai dai kuma minti shida tsakani Marcus Rashford ya kara na biyu sannan ya ci na uku da ya sa United ta hada maki ukun da take bukata.
