Jigawa: Gwamna Badaru Ya Tura Dalibai 100 Kasar Waje Karo Karatu

Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayyana cewa ta kashe kudi har naira miliyan dari Uku, da miliyan tamanin da biyar, da dubu dari biyar, da naira saba’in da biyar (N385, 575, 000) wajen tura dalibai mata su 100 domin yin karatun likitanci a Jami’ar kasar Sudan.

Mai magana da yawun gwamna Badaru, Habibu Kila, ya bayyanawa manema labarai cewa ku?a?en sun hada da ku?in makaranta, wurin zama, da kuma ku?in zirga zirga, da sauran wasu bu?atu.

Sanarwar ta Gwamnati ta biyo bayan ?orafi da ?an adawa ke yi cewa gwamnatin tayi shiru akan abinda ta kashe wajen tura ?aliban kasar Sudan.

?an adawan sun kuma cewa maimakon a ri?a kashe ku?a?en talakawa masu yawa a kasashen waje, gwara a gyara makarantun na cikin gida.

Related posts

Leave a Comment