Ganduje Ya Karbi Ragamar Jagorancin Jam’iyya Mai Mulki Ta Kasa APC

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa sabon shugaban jami’iyar APC mai mulki, Abdullahi Ganduje, ya ce zai kama aiki ba ji ba gani domin tabbatar da jam’iyyarsa ta yi nasara a za?en gwamnan jihohin Kogi da Bayelsa da za a gudanar ranar 11 ga watan Nuwamban 2023.

Ganduje ya bayyana haka ne a yau Alhamis, lokacin da yake jawabi bayan tabbatar da shi a matsayin shugaban jam’iyyar APC, a wajen taron majalisar zartarwar jam’iyyar da ya gudana a Abuja.

An kuma za?i tsohon mai magana da yawun Majalisar Dattijan Najeriya, Ajibola Basiru, ?an jihar Osun a matsayin sakataren Jam’iyar.

A jawabin nasa, Ganduje ya gode wa Shugaba Bola Tinubu, ya kuma jaddada cewa zai tabbatar da zaman lafiyar a cikin jam’iyar.

Ganduje ya yi al?awarin yin aiki tu?uru wajen tabbatar da nasarar jam’iyar a za?en gwamnan a jihohin Kogi Imo da Bayelsa.

Related posts

Leave a Comment