Kungiyar rajin tabbatar da kyakkyawar zamantakewa a tsakanin al’umma wato “Nigerian Institute of Chartered Arbitrators” a turance ta shirya wa Alkalai wani taron kara wa juna ilimi kan yadda za a magance yawan rigingimu dake faruwa a tsakanin al’umma, musanman a yankin arewa.
Taron wanda ya gudana a gidan tarihi na Arewa dake Kaduna ya samu halartar daukacin wasu Alkalan jihar Kaduna ?ar?ashin jagorancin Alkalin Alkalan jihar mai Shari’a Grand kadi Muhammad Danjuma.
Da take zantawa da manema labarai jim ka?an bayan kammala taron shugabar kungiyar ta ?ano da kaduna, Mrs Rosecana G. Ankama tace makasudin shirya taron shine domin ilmantar da Alkalan yadda za a ?auki matakin yin sulhu tsakanin al’umma maimakon yawan shigar da Kara kotu da ke neman zama ruwan dare tsakanin jama’a.
Mrs Rosecana G. Ankama ta ?ara da cewar tana yakinin za a cimma nasara akan taron da suka kira bisa ga goyon baya da ha?in kai da suka samu daga Alkalan.
Wasu daga cikin Alkalan da aka zanta dasu sun bayyana farin ciki akan taron da kungiyar ta kira sannan sun sha alwashin aiki da abin da suka koya domin samun nasarar da ake nema.
