An Yi Kira Ga Osinbajo Da Ya Tsaya Takarar Shugabancin Kasa A 2023

Kungiyar masu ruwa da tsaki da cigaban jam’iyyar APC ta kasa ta yi kira ga mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo da ya taimaka ya fito takarar shugabancin kasa a babban zaben shekarar 2023 domin ?orawa daga inda Buhari ya tsaya.

Kungiyar ta kuma bukaci jigo a jam’iyyar APC na Kasa tsohon Gwamnan Jihar Legas Bola Tinubu da ya janye aniyarsa ta neman tsayawa takarar shugabancin kasa ya ba Osinbajo dama domin nasarar Jam’iyyar gaba daya.

Kungiyar ta yi wannan kiran ne a yayin wanin gagarumin taron manema labarai da ta kira a babban birnin tarayya Abuja ranar Laraba.

Shugaban kungiyar Ahmed Muhammad da Sakataren Kungiyar ?ungiyar Dr. Eberechukwu Eli Dibia, sun ce ?ungiyar tasu wacce take da wakilci a dukkanin fa?in kasar Najeriya, kwanan nan za ta yi wani gangami na yin kira ga ‘yan Najeriya da su marawa takarar Osinbajo baya.

Sun kara da cewar hanya guda da zata taimaka wajen cigaba da ayyukan alheri da Buhari ya samar shine marawa Osinbajo baya ya dora, kasancewar dashi aka fara.

“Hakika babban burin shugaban kasa da jam’iyyar APC shine karasa ayyukan da gwamnatin tarayya ta sanya a gaba yanzu, kuma wanda ya fi cancanta ya jagoranci tafiyar shine Osinbajo, bisa ga haka muna kira ga Tinubu da ya hakura da yin takara ya bada dama ga mataimakin Shugaban Kasa”.

Muna sane da irin goyon bayan da manyan kasa suke dashi ga Osinbajo bisa ga jajircewarshi, mutane irin su mai Martaba Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar wanda ya yabi Mataimakin Shugaban kasar akan hangen nesa da biyayya ga Shugaban kasa, wanda ba za’a manta da shi ba.

Tsayawa takarar Osinbajo wani al’amari ne mai muhimmanci, domin dukkanin abin da ake bukata ga shugaba Osinbajo yana dashi, kuma zai dace da muradun mafiyawancin ‘yan Najeriya bangaren ilimi da shekarun sa.

A bangaren Tinubu yana matsayin babban jigo uban tafiya a jam’iyyar, wanda bada shawarwarin shi za su taimaka matuka, amma yunkurin shi na tsayawa takara na iya haifar wa jam’iyyar da tarnaki.

Babu shakka Najeriya ta tsinci kanta a halin da take ciki yanzu biyo bayan ginin da shugabannin baya suka yi mata, kuma ba domin samun jajartattun mutane irin Buhari da Osinbajo ba da Allah kadai ya san makomar ?asar a yanzu, bisa ga haka Osinbajo ne ya fi dacewa ya ?ora daga inda aka tsaya domin kai kasar ga tudun mun tsira.

Related posts

Leave a Comment