Rahotannin dake shigo mana daga birnin Jos na Jihar Filato na bayyana cewar ana hana al’ummar Hausa/Fulani ganin Likitia a asibitin koyarwan jami’ar Jos saboda suna ikirarin cewa sun yan asalin jihar Filato ne, sannan a tilastasu canza sunan jihohinsu.
Mutane sun dade sun korafin wannan abu dake gudana a asibiti koyarwa na Jami’ar Jos JUTH gabanin bayyanar bidiyo dake nuna wata ma’aikaciyar asibitin tana tabbatar da hakan.
Asibitin JUTH dai ta gwamnatin tarayya ce ba ta jihar ba. Daily Trust ta ruwaito cewa ta samu ji daga bakin wasu marasa lafiya da suka fuskanci wannan lamari yayinda suka je rijista.
Idan mutum yaje rijista, ana bashi fam ya cika inda zai rubuta sunansa, kabilarsa, jiharsa na asali da karamar hukumarsa.
Amma idan Hausa/Fulani Musulmai suka rubuta su yan asalin jihar Filato ne, sai ace musu su canza saboda babu Hausa/Fulani a tarihin jihar.
Hakan ya tilasta wasu canza asalinsu zuwa Kano, Bauchi ko wata jihar Arewa domin samun biyan bu?atar ganin likita.
A bidiyon, an ji ma’aikaciyar na cewa: “Jiharka ta asali daban take da jihar da kake zama. Misali, ni yar Ogbomosho a jihar Oyo ce, kuma kakkani na a Filato aka haifesu, shin zan ce ni yar Filato ce? A’a, da jihar Oyo zan yi amfani.”
“Dalili shine idan muka fara rubuta bayanin cikin komfuta, kuma mutum Hausa/Fulani yace shi dan Filato ne kuma dan Jos ta Arewa, komfutar zata mutu.” “A na’urar, kabilu hudu kadai ke Jos ta Arewa; Jarawa, Naraguta, Buji da Berom.
Domin tabbatar da gaskiyar wannan zargi da ake yiwa asibitin, wani wakilin jaridar Daily Trust yayi basaja ya shiga asibitin matsayin mara lafiya.
Bayan karban Fam, jami’in asibiti ta tambayesa: “Kai ba dan Filato bane. Kai dan Bauchi, Kano, Kaduna ko Sokoto ne ko?” Sai ta sake tambayara mahaifinsa dan wani gari ne, yace mata Jos, Filato.
Sai ta sake tambaya Kakansa dan wani gari ne yace Jos. Sai tace sam, karya yake. Tace: “Zan koreka idan baka fada min gaskiya ba. Ai mun fada muku tun kan mu fara.”
Gabanin dan jaridan, an kori wasu mata, kuma sai da suka canza jiharsu daga Filato suka mayar da shi Kano suka samu ganin Likita.
Sai dai a ?angaren hukumar Asibitin ta karyata labarin, Jami’ar hulda da jama’a ta asibitin, Mrs Bridget Omini, ta ce abinda aka gani a bidiyon ba da sa hannun asibitin bane. Tace: “Ina mai bayyana cewa asibitin koyarwan jami’ar Jos mallakin gwamnatin tarayya ce dake da hakkin kula da kowa, ba tare da banbancin kabila ko addini ba.”
