Tsohon Shugaban ?asa na mulkin soja, Janar Yakubu Gowon, ya bayyana cewa sai mutumin ?warai, sahihi ya kamata ya shugabanci Najeriya a 2023, ba rubabi-rubabi ba.
Gowon ya furta haka ne a ranar Juma’a, lokacin da ?ungiyar Tallata Takarar Mataimakin Shugaban ?asa Yemi Osinbajo ta kai masa ziyara a gidan sa da ke Asokoro, Abuja.
?ungiyar mai suna Progressive Consolidated Group, sun Kai masa ziyarar ce domin su sanar da shi aniyar su ta ganin cewa za?en Osinbajo shi ne mafita kuwa hanyar fidda Najeriya daga ?uncin da ‘yan ?asar ke ciki.
Gowon ya ce duk da ba ya yin katsalandan cikin harkokin siyasa, amma bai ba zai ?i yi wa ‘yan Najeriya nasiha ba cewa wajibin dukkan kowa da kowa ne su ga cewa sun ha?a kai an samu ci gaba, zaman lafiya da shugabanni nagari daga sama har ?asa.
Yayin da Gowon ke bayani, ya ce ya kamata a sani cewa duk sharri da tuggu da ?ulle-?ullen da za a yi don a hana wani nasara, to Ubangiji ne ke ?addara wanda zai yi mulki.
Ya kuma ja hankulan masu kafafen ya?a labarai su fi maida hankali wajen tabbatar da ha?in kan ?asar nan.
Sannan kuma ya ce ba za a kai gaci ba har dai masu neman mu?amai wato ‘yan siyasa sun cusa kishi su da magoya bayan su, maimakon a ri?a ?in bada ?arfi wajen neman mu?amai wurjanjan.
Tawagar da ta kai wa Gowon ziyasa na ?ar?ashin Baraden Lafiya, Musa Kwande da Babban Kodinetan PCG, Ahmed Kari.
Bayan yin jawabai sun kuma gana asirce da Gowon.
