Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar DCP Abba Kyari ya nemi hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta biya shi diyyar naira miliyan 500 kan zargin kama shi da tsare shi ba bisa ka’ida ba.
Kyari, a cikin karar da ya shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/182/22, ya kuma nemi kotu ta umurci NDLEA da ta bashi hakuri ta hanyar rubutu a jaridun kasar guda biyu domin wanke shi daga dukkan zarge zarge.
A cikin karar da ya shigar ta hannun lauyansa, C. O. Ikenna, Kyari ya kuma nemi umarnin: “Hana wanda ake kara (NDLEA), jami’anta, jami’an tsaro, ‘yan sanda ko duk wanda ke wakiltar su daga ci gaba da cin zarafi, tsarewa, tsoratarwa, da kama mai kara ba bisa ka’ida ba.
“Muna bukatar Kotu ta bada umurnin wanda ake kara da ya biya diyyar N500,000,000.00 (naira miliyan dari biyar) ga wanda ke kara, kan tauye hakkin wanda ke kara wanda yake a sashi na 35 da 36 na kundin tsarin mulkin Najeriya (kamar yadda aka gyara).”
Ya kuma bukaci a ayyana kama shi da ci gaba da tsare shi da NDLEA ke yi ba tare da kai shi gaban kotu ba tun daga ranar 12 ga watan Fabrairu har zuwa yanzu a matsayin wanda baya bisa ka’ida da kuma tauye masa yancinsa.
Ya ce sashe na 35(1) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) da kuma sashe na 6 na dokar kare hakkin dan Adam da jama’a ta Afirka ta tabbatar da yancinsa da kuma damarsa ta yin walwala.
