Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi wani taron sirri gwamnonin APC a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Talata.
Shugaban gwamnonin APC, Gwamna Atiku Bagudu, na jihar Kebbi, shi ne ya jagoranci takwarorinsa zuwa wurin Buhari. Wannan ganawa na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar APC ke cigaba da fa?i tashin zakulo mataimaki ga ?an takarar shugaban ?asa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Taron ya samu halartar shugaban ma’ikatan fadar gwamnatin tarayya, Farfesa Ibrahim Gambari, da Sakataren gwamnati, Boss Mustapha. Haka nan kuma a ?aya ?angaren gwamnonin da suka je wurin taron sune, Babagana Zulum na Borno, Nasir El-Rufai na Kaduna, Abdullahi Sule na Nasarawa, Badaru Abubakar na Jigawa. Sauran sune, gwamna Simon Lalong na jihar Filato, Yahaya Bello na jihar Kogi da kuma gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo.
