?an takarar kujerar Gwamnan jihar Kaduna karkashin jam’iyyar APC Alhaji Sani Sha’aban, ya bayyana abin da ya farus APC a Jihar da sunan za?en fidd gwani, da ?auki dora kuma wasan kwaikwayo ne da ba za a lamunta dashi ba.
Sani Sha’aban ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya fitar yana mayar da martani dangane da abin da ya faru da sunan za?en fidda gwani a Jihar.
?an siyasar ya bayyana karfa da gwamnatin jihar ta yi wanda ya kai ga ayyana Uba Sani a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na Gwamna a matsayin son zuciya na giyar mulki da gajeren tunani akan abin da zai je ya dawo a jam’iyyar.
“Kamar yadda ya ke bisa ga tsari da doka, jami’ai daga hukumar INEC suke da alhaki akan takardun gudanar da za?e, da kuma sa ido akan yadda za?e ya kamata ya kasance, amma a jihar Kaduna ba a samu hakan ba gwamnati ce ta raba takardun zaben”.
Dangane da batun wakilan Jam’iyya masu zabe wato Deligates, ?an siyasar ya ce wannan shine mafi muni na abin da ya faru domin an kwashe Deligates an kai su Otel an rarraba musu ku?i sun yi gaba, sannan aka dauko wasu mutane na daban suka yi wasan kwaikwayo da sunan za?en fidda gwani bisa shiryawar gwamnatin jihar, aka tozarta asalin wa?anda ya kamata su gudanar da za?e.
“Wannan abin damuwa da takaici ne ga jiha kamar Kaduna jihar da na fito, kuma karan tsaye ga tsarin mulkin dimokura?iyya, da yunkurin hana wasu yin takara ba a matakin kujerar Gwamna kawai ba, a dukkanin Kujerun siyasa na matakai daban daban tun daga kan majalisar jiha tarayya da ta Dattawa.
Sani Sha’aban ya rufe bayanin shi da cewar ko ka?an bai amince da wannan kwamacala da aka yi da sunan za?en fidda gwani ba, kuma nan ba da jimawa ba zai bayyana matakin karshe da za su ?auka.
