Masarautar Oyo Ta Yi Gagardi Kan Kusantar Matan Marigayi Alafin

Labarin dake shigo mana daga Ibadan babban birnin jihar Oyo na bayyana cewar ana cigaba da zaman makoki biyo bayan rasuwar Oba Lamidi Adeyemi lll, Alaafin na Oyo wanda ya mutu bayan shekaru 52 a karagar mulki.

Rahotanni sun bayyana cewar Oba Adeyemi mai shekaru 83 ya bar gidan duniya a daren Juma’a bayan jinyar da ya sha a asibitin Afe Babalola dake Ado Ekiti babban birnin jihar Edo.

Oba Lamidi na matukar kaunar mata, musamman kyawawa masu jini a jika, bai taba boye wannan batun ba, ya rasu ya bar mata 13 masu jini a jika.

A tattaunawar da BBC Yoruba tayi da Chief Ifayeki Elebuibon mai magana da yawun masarautar ya bukaci mazan dake hararo matan sarkin da su kara hakuri. A cewarsa, har yanzu matan na takaba.

Ya ce, ba mai iya aurensu har sai sun gama takabar marigayin basaraken, kuma babban abu ma, har sai an fitar dasu daga takaba a al’adance.

Matan marigayin sarkin na da damar auren duk wanda suka ga dama, amma dole sai anbi matakan da al’ada ta tanada kafin su auru. Bayan an cire musu kafin da Alaafin din ya musu.

Daga nan ne za su jira sabon sarki. Idan sabon sarkin na da ra’ayin zama dasu, zai cigaba da zama mijinsu, idan kuma bai da bu?ata shikenan.

Related posts

Leave a Comment