Dan Bindiga Ya Fi Deligate Imani – Shehu Sani

Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya ce babu maraban ?an bindiga da ‘Deliget’ a siyasan Najeriya.

Shehu Sani ya bayyana cewa yadda mahara ke kar?ar ku?i a hannun wa?anda suka yi garkuwa da haka suma ‘Deliget’ ke karvar irin wannan ku?ade a hannun mutane da sunan wai za su zabe su.

” Na shiga siyasa ne domin a gyara tsarin a tsaftace shi ta yadda za a rika za?en nagartattun mutane wa?anda suka cancanta ta hanyar yin za?en mai aminci da nagarta tun daga za?en ?an takara zuwa za?en shugabanni.

” Ni fa a ganina ban fa?i zaben fidda gwani ba, ban yi nasara ne a kasuwanci siye da siyarwar ?an takara ba ta hanyar wanda yafi zabga ku?i ya kwashi dami.

” Bai kamata ace wai ta irin wannan hanya ce za a ri?a za?en wa?anda za su shugabanci jama’a a kasar nan ba, saboda maimakon a za?i nagari mai dammai a aljihu ne za a baiwa mulki ko mai lalacewar sa kuwa. Hakan bai dace ba.

” Gaba ?aya turbar siyasar kasar nan a gur?ace ta ke, hanyar za?en ?an takara ta hanyar zabe na ‘Deliget’ hanya ce kawai da ya bada damar dora ru?a??u, gurbatattun ?an siyasa karagar mulki cikin sauki ta hanyar watandar miliyoyin ku?i.

” Idan ba mun dawo daga rakiyar siyasar mai-kudi-?auka bane komai munin sa ba za mu taba ?an?aro ?asar nan daga bangon ginin cuwacuwa, almundahana, karfakarfa ba, sannan kuma matasa sai dai su ji a salansa amma ba wai su iya shiga a fafata da su ba.

Related posts

Leave a Comment