Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa, Muhammadu Buhari, ya amince da na?in tsohon shugaban hukumar za?e, INEC, Farfesa Attahiru Jega, a matsayin shugaban majalisar gudanarwa na jam’iar Jos (UNIJOS).
Ministan ilimi, Adamu Adamu, wanda ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja, yace Buhari ya amince da na?in shugabannin jami’o’in tarayya 42 dake fa?in ?asar nan, kuma aikin nasu ya fara aiki nan take.
Shugaban ya kuma amince da na?in biyu daga cikin tsofaffin ministocinsa, Prof Anthony Anwuka da Udoma Udo Udoma, a matsayin shugabannin majalisar zartarwa a wasu jami’o’i.
Yayinda da Anwuku zai jagoranci majalisar jami’ar albarkatun man fetur dake Effurum, jihar Delta, shi kuma Udoma zai jagoranci ta jami’ar Bayero dake Kano.
Hakanan kuma shugaba Buhari ya amince da na?in shugabannin jami’o’i (Chancellors) mallakin gwamnatin tarayya. Adamu, yace:
“Kamar yadda mukasan iyayen mu sarakuna suke yi, muna fatan wa?annan shugabannin su zama masu kyautatawa jami’ar da aka tura su.” “An ?auke su daga yankin da suke gudanar da mulkinsu zuwa wani wuri na daban kuma muna fatan wa?annan na?e-na?en zasu taka rawa wurin ?ara dan?on zumunci tsakanin al’ummar Najeriya.”
