Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya shawarci wasu sassan Najeriya su rika yiwa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari adalci alal akalla. Masari wanda ya siffanta gwamnatin Buhari a matsayin mafi jin kan talaka tun lokacin da aka kafa a Najeriya a 1914, ya ce yan Najeriya su godewa irin nasarorin da aka samu a tattalin arzikin tun 2015 da Buhari ya hau mulki duk da faduwar danyen mai a kasuwar duniya.
Masari ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a taron kaddamar da zaman mutanen da suka amfana da shirin ciyar da dalibai da gwamnatin tarayya ke yi a jihar Katsina.
“Wajibi ne muyi godiyan cewa tun lokacin da aka fara gwamnati a Najeriya, ba’a taba gwamnatin da ta taba rayuwar talakawa irin wannan gwamnati ba.”
“Mutane kawai na magana ba tare da ganin irin kokarin da akeyi ba.” “Ko kun so, ko kun ki, shi (Buhari) ya kawo sauyi shugabanci ta yadda ko mutumin da bai taba sanin gwamnati ba yana amfana da ita.
Masari ya kara da cewa gwamnatin tarayya a kulli yaumin tana ciyar da akalla dalibai 800,000 a jihar Katsina, kuma wannan shiri na cin kudi sosai.
