An bayyana cewar kirkiro da ‘yan sandan jihohi zai taimaka matuka wajen samar da tsaro da ya da?e yana addabar Najeriya musamman yankin Arewacin kasar dake fuskantar barazanar ‘yan Bindiga a Kullum.
?ungiyar Dattawan Arewacin Najeriya wato Northern Elders Forum ta bayyana hakan, inda tace tana goyon bayan yun?urin ?an majalisar dokokin ?asar ke yi wajen zartar da dokar da za ta bai wa jihohi ikon kafa rundunar ?an sanda ta jiha.
Tuni dai aka yi wa ?udurin dokar karatu na biyu a majalisar wakilai.
An dade ana ta?addama a kan batun kafa ?an sandan jihar, sakamakon zargin da wasu ke yi cewa gwamnoni za su yi amfani da su wajen ya?ar abokon hamayyarsu.
Sai dai a tattaunawar da akayi da Kakakin kungiyar Dattawan Arewan, Dr Hakeem Baba Ahmed ya ce ?an sandan za su taimaka wajen inganta tsaro idan aka bi tsari wajen kafa rundunonin nasu.
