Za Mu Sabunta Ayyukan Ta’addanci A Najeriya – Tsagerun Naija Delta

?ungiyar tsageru ta yankin Neja-Delta a kudancin Najeriya mai suna Niger Delta Avengers ta yi barazanar ci gaba da kai hare-hare a kan matatun man fetur na ?asar da kuma ‘yan siyasar yankin da ke “ha?a kai da gwamnati”.

Wata sanarwa da ?ungiyar ta wallafa a shafinta na intanet ta ce gwamnatin Najeriya ta “ta sha yin buris da bu?atunta”.

?ungiyar ta ta?aita ayyukan ha?ar mai a Najeriya a 2016 sakamakon hare-hare da ta dinga kaiwa, ciki har da wanda ta kai kan wani bututun mai na ?ar?ashin ruwa.

Tun daga lokacin ne kuma ta dinga yin barazanar kai hari amma ba ta yi hakan ba tun 2017, a cewar kamfanin labarai na Reuters.

“Gwamnatin Najeriya ta sha yin buris da bu?atunmu da kuma halin da ?asar ke ciki,” a cewar sanarwar. “Duk bututun da muka tsara kai masa hari ba za mu ?yale ba sai mun lalata.”

Barazanar tasu na zuwa ne yayin da majalisar tarayya ke muhawara kan kasafin ku?in da ya kamata a dinga bai wa yankunan da ake ha?o man da zummar yi wa dokokin man fetur ?in ?asar babbar kwaskwarima.

Al’ummomin yankunan na son a dinga ba su kashi 10 cikin 100 na ku?in man da aka ha?o mai maimakon 2.5 da ake ba su a yanzu.

Related posts

Leave a Comment