EFCC Ta Gurfanar Da Okorocha Gaban Kuliya

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wata Kotun Tarayya ta ba wa hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar ta’annati umarnin rike tsohon gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha, a hannunta.

Mai Shari’a Inyang Ekwo ya bayar da umarnin tsare shi a hannun EFCC bayan hukumar ta gurfanar da shi a gabansa bisa zargin almundahana.

Kazalika ya ?age zaman kotun zuwa ranar Talata domin sauraren bukatar bayar da belin Sanata Okorocha, wanda yanzu yake wakiltar Yammacin Imo a Majalisar Dattawan kasar,

Ana tuhumar Rochas da laifuka 17 da ke da alaka da zargin wawure naira biliyan biyu da miliyan dari tara.

Related posts

Leave a Comment