Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce shi bai da matsanancin burin dole sai ya zama shugaban kasa a za?en 2023.
Jagoran jam’iyyar NNPP na ?asa ya yi wannan furucin ne yayin zantawa da kafar watsa labarai Channels tv ranar Litinin 30 ga watan Mayu, 2022.
Ya ce shi da kuma masu kyakkyawar zuciya sun shiga Jam’iyyar NNPP ne domin canza halin da ake ciki da kuma ceto Najeriya daga rushewa.
“Abin da yan Najeriya ke cewa shi ne suna bukatar nagari a kowane lokaci, ni zan iya baku tabbacin cewa Ni ba mutum bane da ya matsu dole sai ya zama shugaban ?asa.”
“Mun gaji da tsohon tsarin da ake amfani da shi yau, shiyasa muka rungumi NNPP domin kawo canji, yadda abubuwa ke wakana a kasar nan yanzu ya yi muni.” “Kowane mutum ya damu da halin tsaro, tattalin arziki ya raunata, dukan sassan ilimi da al’adu, komai dai ya lalace.
Haka ne ma?asudin da ni da makamanta na muka shiga NNPP, muna bukatar ha?uwa wurin ?aga kudu da arewa”.
