Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar za?e mai zaman kanta ta ?asa INEC da Hukumar Yaki da Rashawa ta EFCC tare da sauran masu ruwa da tsaki sun fara wani zama domin tattauna batun rashawa da aka samu a babban zaben Najeriya na 2023.
Tawagar, wadda cibiyar ‘The Conversation Africa’ ke ?aukar nauyin su kamar yadda ta tsara gudanar da irin wadannan taruka domin tattauna tsarin shugabanci.
A cewar sanarwar, sauran mutanen da ake zama da su sun hada da kungiyoyin farar-hula da kungiyar Code4Afrika da dai sauransu.
Ana sa ran bayan kammala zaman a fito da batutuwa na zarge-zarge da ake ta yi kan rawar da rashawa ta taka a za?en Najeriya da kuma sauran kalubale da ake zargi.
A ranar Litinin ne Kotun Sauraron ?ararrakin Za?en Shugaban ?asa ta fara zama domin sauraron ?arar da ?an takarar jam’iyar PDP, Atiku Abubakar da na jam’iyar Labour, Peter Obi su ka shigar.
?an takarar na ?alubalantar za?en Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe za?en shugaban ?asa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Nahiyar mu ta Daily Nigerian ta rawaito cewa Hukumar Za?e Mai Zaman Kanta ta ?asa (INEC) ta bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe za?en.
A za?en, Tinubu ya samu kuri’u 8,794,726 inda ya doke tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku, wanda ya samu kuri’u 6,984,520 da Peter Obi, wanda ya samu kuri’u 6,101,533.
A cikin ?an takarar da ke ?alubalantar nasarar Tinubu, Obi da Atiku ne suka fi fice.
Daily Trust ta gano cewa kotun ta yi cikar-kwari da lauyoyi da kuma magoya bayan ?an takarar.
Chris Uche, SAN, shi ne shugaban kungiyar lauyoyin da za su kare Atiku yayin da Wole Olanipekun (SAN) ke jagorantar na Tinubu, sannan Levi Uzoukwu (SAN) shi ne shugaban tawagar Obi.
