An fa?a wa za?a??un gwamnonin da za a rantsar ranar 29 ga watan Mayu a Najeriya, cewa a cikin nasarar shugabanci, akwai ?arasa ayyukan da magabatansu, suka faro.
Matakin zai taimaka wajen tabbatar ci gaban ?asa da alkinta dukiyar al’umma da rage kashe ku?i wajen gudanar da harkokin mulki a matakan jihohi.
Wannan jan hankalin, na cikin ?umbin bayanai da shawarwari da aka gabatar wa za?a??un gwamnonin Najeriya, yayin wani taron sanin makamar aiki da aka shirya musu a babban birnin ?asar, Abuja.
Manufar taron na kwana uku, ita ce shirya gwamnonin masu jiran gado da dabaru da hikimomin shugabanci kafin a rantsar da su nan da kwana 12.
?ungiyar gwamnoni ta Najeriya ce ta shirya taron a Abuja, inda ta gayyato ?wararru a fannoni daban-daban game da sanin dabarun shugabanci a ciki da wajen ?asar domin bun?asa ?warewar sabbin gwamnonin.
Jiga-jigan ‘yan siyasa kamar Simon Lalong na jihar Filato da Nasiru El-rufa’i da su Kayode Fayemi sun ja hankalin za?a??un gwamnonin da za su hau karagar mulkin jihohi su fifita muradan al’umma a kan bambancin siyasa da ta a?ida.
Haka zalika, an ja hankalin sababbin gwamnonin kada su yi ?asa a gwiwa wajen koyon dabaru da salon ayyukan raya ?asa daga wasu jihohi, don hanzarta ci gaban jihohinsu.
?aya daga cikin mahalarta taron, za?a??en gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Ahmed Aliyu ya ce horon sanin makamar aikin, ba shakka zai taimaka wajen inganta gudanar da harkokin mulki a jihohi da zarar sun fara aiki.
Ya ce “kusan in ce mun koma aji. Don aji ne ake shiga tun bakin ?arfe 9 na safe zuwa 9:30, wata ran a kai ?arfe 4 ko 5 na yamma”.
A cewar Ahmed Aliyu, duk da yake ya yi mataimakin gwamna tsawon shekara hu?u, kuma ya sha gudanar da ayyukan da gwamna ke yi, amma ya koyi sabbin dabaru da bai ta?a samu ba a baya.
“Musamman an nuna mana muhimmancin ?arin hanyoyin samun ku?in shiga a jihohinmu.
Kuma an ja kunnenmu game da bu?atar kammala ayyukan da gwamnoni masu barin gado suka faro, saboda da ku?in jihohinmu ake yinsu”, in ji za?a??en gwamnan na Sokoto.
A ranar 29 ga watan Mayun nan ne, za a rantsar da su, bayan za?en gwamnoni a ranar 18 ga watan Maris.
