Shugaban ?asa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da gwamnan babban bankin ?asar – CBN Godwin Emefiele daga mu?aminsa.
Sanarwa daga ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayyar ?asar ta ce an dakatar da gwamnan CBN ne domin a gudanar da bincike sannan kuma ya sauya fasalin harkokin ku?i a ?asar.
“Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da gwamnan babban banki, Mr Godwin Emefiele, CFR daga ofis ba tare da bata lokaci ba,” in ji sanarwar.
An umurci gwamnan CBN din ya mika ragamar tafiyar da harkokin ofis din ga mataimakin gwamna mai kula da harkokin gudanarwa wanda zai kasance mukadashin gwamna har sai an kammala bincike da kuma sauye-sauye a bangaren ku?i.
Matakin da shugaba Tinubu ya dauka na zuwa ne kasa da mako biyu da aka rantsar da shi a matsayin shugaban kasar.
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ne ya na?a Emefiele a matsayin shugaban CBN a shekara ta 2014.
Ya ci gaba da zama shugaban babban bankin na Najeriya har ?arshen wa’adin mulki na biyu na tsohon shugaban ?asa Muhammadu Buhari.
Sai dai wasu matakai da ya ?auka gabanin babban za?en Najeriya na 2023 ya janyo ce-ce ku-ce mai yawa a ?asar.
Batun sauya fasalin ku?i da bankin ya ?addamar ya haifar da ?arancin ku?i a hannun al’umma, wani abu da ya janyo wahalhalu da dama.
Sai dai Emefiele ya ce sauya fasalin ku?in wani yun?uri ne na ya?i da rashawa da matsalar tsaro da kuma ?abba?a tsarin rage amfani da tsabar ku?i tsakanin al’umma.
Amma lamarin bai yi wa Bola Tinubu da?i ba, wanda a lokacin yake takarar shugaban ?asa.
