Rahoton dake shigo mana daga jihar Katsina na bayyana cewar Kwantrolan hukumar Kwastam dake jihar Wada Chedi, ya yi bayanin dalilin da yasa jami’an hukumarsa suka gaza hana fasa kwabrin haramtattun kayayyaki ta jihar.
Chedi ya bayyana cewa akwai hanyoyi da yawa da masu fasa kwabrin ke amfani da shi wajen shigo da kayayyaki. Najeriya na iyaka da Nijar ta karamar hukumar Jibia dake jihar Katsina.
Kwantorola Wada Chedi ya bayyana haka a taron masu ruwa da tsaki ranar Alhamis a jihar Katsina.
Kwantrolan yace adadin jami’an kwastam dake Najeriya ba zai isa hana shigo da kaya ba. Yace: “Ba zai yiwu hafsoshinmu su mamaye ko ina ba ko da za’a kwaso dukkan jami’an kwastam na Najeriya, ba zamu iya tare dukkan hanyoyin shiga ba, shiyasa muke son jama’a su taimaka mana da bayanai kan masu fasa kwabri.”
“Akwai hanyoyin shiga 12 a jihar Katsina amma yanzu, akwai sama da hanyoyi 100 da mutanen nan ke amfani wajen shigo da kayayyaki.” Ya kara da cewa masu fasa kwabri na da dabaru daban-daban wajen gujewa jami’an tsaro.
Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Mustapha Inuwa, ya ce rufe iyakokin Najeriya bai hana shigo da haramtattun kayayyaki ba har yanzu. Ya yi kira ga jami’an kwastam su duba halin da al’ummar jihar ke ciki su bude iyakokin.
