Yayin da ake ci gaba da ta?addama kan wa’adin da babban banki ya bayar na daina amfani da tsofaffin ku?i, gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya ya ce dukkanin takwarorinsa na goyon bayan ?arar da aka shigar na soke wa’adin.
Gwamnonin, wa?anda suka hada da na jihohin Kaduna da Zamfara da kuma Kogi sun bu?aci kotun kolin ta taka wa babban bankin burki game da wa’adin.
A tattaunawarsa da BBC, gwamnan jihar Gomben, ya ce tsarin da CBN ?in ya kawo ba zai yi wa al’ummar arewacin ?asar da?i ba ganin cewa bankuna ba su wadata yanda komai zai tafi daidai ba.
Ya ce ba a fa?a wa shugaban ?asa gaskiya ba kan abubuwan da ke faruwa na harkokin banki a arewa sannan kuma ba su buga isassun takardun ku?i da za su wadaci al’umma ba.
”Ya kamata in ka kawo ku?inka koda dubu biyar ne a canza maka su a take, in kuma ba haka ba, bu?atar da muka ce shi ne a bar wa?annan takardun ku?in kala biyu su tafi har zuwa wani lokacin da babban bankin zai iya tanadar isassun takardun ku?i,” in ji gwamnan.
Ya ce abin da ya sa suka kalubalanci wannan tsari ba wani abu ba ne illa su ne suke kusa da al’umma kuma suka san matsalar da suke ciki ba wai domin bu?atar kansu ba.
Gwamnan ya ce tun shekarar da aka kawo tsarin cewa duk wani banki na kasuwanci sai yana da jari na biliyan 25, daga lokacin ne arewacin ?asar ya fita daga tsari na bankuna na Najeriya.
Ya yi i?irarin cewa akasarin masu iko da bankunan ?asar sun fito ne daga kudancin ?asar.
Ya ce babu network a yawancin ?auyuka da mutane za su iya amfani da shi wajen tura ku?i sannan mutane ba su da ilimin yanda ake tura ku?a?e, wanda ya ce hakan zai sanya masu rayuwa a irin wa?annan wurare su gaza bu?e asusun ajiya a banki.
