Rahotanni daga Jalingo babban birnin Jihar Taraba na bayyana cewar Mutum takwas cikinsu har da ?an Basarake yan bindiga suka sace a kauyen Illela, ?aramar hukumar Karim – Lamido a jihar Taraba.
An ruwaito cewa yan ta’adda da suka kai adadin mutum 15 sun farmaki ?auyen da misalin ?arfe 4:00 na yammacin ranar Alhaamis. Rahotanni sun bayyana cewa maharan wani bangare ne daga cikin tawagar yan bindigan da suka addabi yankin a yan watanni kalilan da suka gabata.
Wani mazaunin yankin da abun ya faru, Dauda Suleiman, ya shaida wa yan jarida ta wayar salula cewa yan bindigan sun yi awon gaba da mutum 8 cikinsu har da dan Basaraken garin, sun tafi da su zuwa wurin da babu wanda ya sani.
Suleiman ya ?ara da cewa a halin yanzu yan bindiga ne ke da iko da yankin, suna yawo ?auke da bindiga ba tare da wani yace musu uffan ba, da rana ko da dare. A cewarsa babu wasu jami’an tsaro a ?auyen, a koda yaushe mutane maza da mata na fama da fashi da kuma garkuwa.
Suleiman ya ce: “Yanzun yan bindigan ke da ta cewa a yankin, sun tilasta wa mutane da dama barin gidajensu.”
Hakimin Zip, Alhaji Uba, ya shaida wa manema labarai cewa ?ansa na cikin mutum takwas da maharan suka yi garkuwa da su, kuma sun nemi miliyan N70m ku?in fansa.
Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, bai ?aga kiran wayar da aka masa ba balle jin ta bakin yan sanda.
