Kano: Dalilan Kotu Na Damka Ragamar APC Bangaren Ganduje

Kotun daukaka kara ta kwace shugabancin jam’iyyar APC ta Kano daga bangaren sanata Ibrahim Shekarau zuwa bangaren gwaman Abdullahi Ganduje wato karkashin shugabancin Abdullahi Abbas.

Idan ba a manta ba kotu a Abuja ta kwace shugabancin jam’iyyar APC daga hannu bangaren Ganduje zuwa bangaren Sanata Ibrahim Shekarau da ta zabi Haruna Danzago a matsayin shugaban jam’iyyar ta jiha.

Kotun daukaka kara ta ce kotun da ta yanke wancan hukunci bata yi daidai ba domin bata da hurumin yanke hukunci da sauraren karar ma tun daga farko.

Kotun ta ce doka bata amince akai ga sai an bayyana gaban kuliya ba kafin a warware tarzoma irin haka wanda ta shafi rikicin cikin gida.

A dalilin haka kotun ta ce jagorancin jam’iyyar APC a jihar Kano dole ya koma ga bangaren su Abdullahi Abbas wanda shine gabadaya ya’yan jam’iyyar a wancan lokaci suka amince shugaban jam’iyyar ba tare da an yi zabe ba.

Related posts

Leave a Comment