Dalilin Da Ya Sa Ba Ma Kama ‘Ya’yan Masu Kudi – Hisbah

Hukumar Hisbah a jihar Kano a Tarayyar Najeriya ta yi karin bayani kan zargin da ake mata na bada fifiko kan hukunta marasa karfi, a jihar ta Kano.

Hakan dai ya biyo bayan korafe-korafen da wasu suka rika yi musamman a kafafen sada zumunta ciki da wajin jihar.

Al’umma da dama sun zargi hukumar da kau da kai daga abin da masu mulki da masu kudi ke yi.

Kan hakan ne Gidan radio Freedom ta tuntubi Babban Daraktan hukumar ta Hisbah Dr, Aliyu Musa Aliyu Kibiya.

Dr Aliyu Kibiya, ya ce Hisbah tana yin da’awa ga kowa da kowa sai dai a bisa mataki, mataki

Saboda haka, irin salon da ake yiwa gama garin mutane, ba shi ne wanda za a yiwa manyan mutane ba.

Ya ci gaba da cewa Mu yadda mu ke yiwa kallon abin in aka ce shugaba ya yi laifi ba tarbiyyar Musulunci ba ce a je masallaci ana fada a lasifika.

Akwai wadanda suna da hanyar da za su samu shugaba su da shi kuma dama aikin shi ne isar da sako shi kuma Allah shi yake shiryarwa.

©Zuma Times Hausa

Related posts

Leave a Comment