Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar dake lura da hasken wutar lantarkin Najeriya (NERC) ta umurci kamfanonin raba wutar lantarki 11 (Discos) su kara farashin wutar daga ranar 1 ga watan Satumba, 2021.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Asabar, hukumar NERC ta ba kamfanonin damar kara kudin ne a wasikar mai taken “Sanarwan Karin Farashi.”
Hakazalika an tattaro cewa a cikin wata takarda mai lamba ”023/EKEDP/GMCLR/0025/2021, kamfanin raba lantarkin Eko (EKEDC), ya sanar da abokanan hul?ar shi cewa za’a yi karin kudin wutar daga ranar 1 ga Satumba, 2021.
“Wannan kari zai bayyana a kan takardar biyan kudin wuta na Oktoba 2021, wanda ke nuna adadin wutan da akayi amfani da shi a watan Satumba.”
“Amma abokanan hul?ar mu masu amfani da Mita, muna kira gareku ku gyara Mitocin zuwa sabon farashin da NERC tayi umurni.”
Yayinda aka tuntubi mai magana da yawun hukumar NERC, bai daga wayarsa ba kuma bai amsa tambayar da akayi masa ta sakon akwatin SMS ba.
Anata bangaren ?ungiyar kwadago ta kasa ta yi fatali da wannan shiri na ?arin kudin wutar da hukumar ke shirin yi, inda ta bayyana shi a matsayin tsagwaron rashin imani.
Mataimakin Shugaban ?ungiyar Kwadago ta ?asa Kwamared Joe Ajaero ne ya sanar da hakan a cikin wata tattaunawa da aka yi dashi ta wayar tarho a Abuja.
Ya kara da cewar akwai rashin tausayi matuka daga bangaren Gwamnati wadda suka gaza biya karancin albashi na 30,000 sannan suke yunkurin kara farashin wutar lantarki.
