EndSARS: Za A Cigaba Da Rubuta Jarrabawar NECO

Hukumar shirya jarabawar kammala karatun sakandare a Nijeriya (NECO) ta sanar da ranar 9 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da dalibai za su cigaba da zaman zana jarabawa a fadin kasar.

Idan za a iya tunawa hukumar ta dakatar da zana jarabawar ne sakamakon zanga-zangar EndSARS da ya rikede zuwa rikici,

Mai magana da yawun hukumar, Azeez Sani ya bayyana cewa za a ci gaba da jarabawar daga ranar Litinin 9 ga watan Nuwamba zuwa ranar Asabar 28 ga watan Nuwamba.

Zanga-Zangar EndSARS wadda ta fara a sashin Kudancin Najeriya a Watan Jiya ta haifar da matsaloli da dama a kasar, inda abubuwa da dama na harkokin gwamnati da na jama’a suka tsaya cak, sakamakon yadda Zanga-Zangar ta sauya manufa.

Related posts

Leave a Comment