Da Yiwuwar Cin Biredi Ya Gagari Talaka – Masu Gidan Biredi

Shugaban masu gidan burodi a Abuja, babban birnin tarayya Alhaji Ishak Aldul-Rahim ya ce yanzu haka tsadar man dizel ta sanya su cikin mawuyacin hali.

Ya ce “Shekaran jiya na sayi man dizel a kan Naira ?ari takwas da talatin kan kowace lita amma daga baya na koma an ce ya zama Naira dubu ?aya da ?ari biyar kan kowace lita, ban san yadda za mu ?are ba,” in ji shi, a hirarsa da BBC.

Baya ga haka nan ya ce man na dizel yana ?aranci a wuraren sayarwa.

A cewar sa baya ga tashin farashin mai, kusan farashin ?aukacin abubuwan da suke bu?ata wajen ha?a burodin sun tashi.

Alhaji Ishak Aldul-Rahim ya ce farashin wasu kayan da suke bu?ata domin ha?a burodi ya ninka har sau uku.

Ya ?ara da cewa “Ina ganin da wuya ne farashin burodin da muke sayarwa 500 ba zai koma dubu ?aya ba.”

Dama dai tuni masu masana’antu suka koka game da hauhawar farashin man na dizel babu ?a??autawa a daidai lokacin da ake fuskantar matsanancin ?arancin wutar lantarki.

Yanzu haka dai ?ungiyar dillalan man dizel ta ce idan hukumomi ba su ?auki matakan da suka dace ba to kuwa farashin man zai zarce Naira dubu ?aya daga farashinsa a hukumance, wato Naira ?ari shidda da hamsin da hu?u.

Mataimakin shugaban ?ungiyar masu masana’antu ta Najeriya Alhaji Ali Sufyanu Madugu ya ce a makon nan an sayi man na dizel a kan kudi Naira ?ari takwas da arba’in zuwa Naira ?ari takwas da hamsin a birnin Kano.

A cewarsa tashin farashin man ya shafi farashin kayan da kamfanoninsu ke samarwa.

Related posts

Leave a Comment