Buhari Bai Da Niyyar Yin Tazarce – Garba Shehu

Kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai nemi zarcewa zango na uku a cikin ofis ba, kuma ba ya sha’awar yin hakan.

A cewar Garba Shehu, wanda ya tattauna da gidan talabishin na Arise TV a ranar Talata, Shugaban kasa yana matukar damuwa kan hare-haren da ake kaiwa ofisoshin INEC da caji ofis din yan sanda kuma a kona su a sassa daban-daban na kasar nan.

Shugaban ya bayyana masu hannu a wa?annan hare-haren a matsayin masu son kawo tashin-tashina.

Hakanan kuma kakakin shugaban kasan, Malam Shehu, ya musanta zargin da wasu keyi cewa hare-haren da ake kaiwa ofisoshin hukumar zabe INEC wani kokari ne na hana zaben 2023.

Wanda idan hakan ta faru shugaban kasa zai cigaba da zama kan madafun iko har sai komai ya dai-daita.

Related posts

Leave a Comment