Labaran dake shigo mana yanzu haka daga Birnin Kano na bayyana cewar Hukumar karbar korafin jama’a da yaki da rashawa ta jihar Kano, PCACC, ta bayyana shirin ta na karya farashin kayan abinci a fadin jihar.
An ruwaito cewa, shugaban hukumar, Mahmoud Balarabe ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Alhamis, inda ya sha alwashin daidaita farashin kayan abinci a fadin jihar gaba ?aya.
“Hukumar ta damu da yadda kayan abinci suka tashi a hannun ‘yan kasuwa wanda hakan ya na wahalar da talakawan jihar.”
Balarabe ya ce hukumar ba za ta tankwashe kafa tana kallon mugayen ‘yan kasuwa suna dora wa jama’a wahala ba, duk da tsananin rayuwar da kasar nan take ciki.
“Yanzu muna aiki a kan korafin jama’a ne da kuma yaki da rashawa. Muna aikin tare da majalisar jihar Kano don ganin sun sanya doka kuma mun tursasa ‘yan kasuwa sun karya farashin kayan abinci.
“Cikin dokokin akwai ci gaba da bincike a kan karin farashin kayan abinci da ‘yan kasuwa su ke yi a fadin jihar. “Ganin halin tsananin rayuwar da jama’a suke ciki, sai mu ka ga ya kamata a ce mun sa ‘yan kasuwa sun daidaita farashin kayan abinci,” a cewar sa dole doka ta tankwasa duk wanda ya yi kokarin bijirewa.
“Dole doka ta zama madubin al’umma. Ba za mu zura ido muna ganin mutane suna yin yadda suka ga dama ba,” a cewar sa.
Balarabe ya bayyana shirin su na ganin sun tankwasa tarbiyyar yara ta hanyar samar da salon koya wa yara sana’o’i a makarantu don su girma da neman na kansu a zuciyoyin su.
