Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Ondo dake kudancin Najeriya na bayyana cewar wasu ?an bindiga sun bu?e wa mabiya addinin Kirista da dama wuta a babban cocin a jihar dake Akure.
Rahotannin sun kuma ce ?an bindigar sun kashe mutane da sace wasu da dama da ba a tantance adadinsu ba a harin na Cocin.
Lamarin da ya faru ranar Lahadi da rana a Cocin mabiya Katolika ta St. Francis da ke bayan fadar sarkin garin Owo, wani babban gari mai tazarar kilomita 40 daga Akure babban birnin kasar.
Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa ‘yan bindiga da dama ne suka mamaye cocin yayin da ake ci gaba da gudanar da ibada.
Ya ce Sun yi harbin kan mai uwa da wabi, inda suka kashe wasu sannan suka yi awon gaba da wasu da ba a tantance adadinsu ba.
