Ha?a??iyar ?ungiyar Matasan Najeriya ta fito fili ta shelanta yin watsi da dukkannin ‘yan takara da manyan jam’iyyu suka tsayar, tare da yin kira na mayar da hankali wuri guda domin za?en Mutum guda wanda zai iya kai kasar ga nasarar.
Da yake jawabi a yayin tattaunawar da ya yi da manema labarai a garin Kaduna Shugaban ?ungiyar Matasan Najeriya Alhaji Abdullahi Abubakar Wali, yace a halin da ake ciki Najeriya na bukatar jajirtaccen Mutum matashi mara tsoro wanda zai tsamo kasar daga halin da take ciki.
“Shi wannan mutumin da muke magana a kanshi kowa ya san shi kuma an san irin kwazon da ya yi a matsayin da ya ri?e a gwamnatin baya, muna da ya?inin zai iya domin shi ya dace wajen ceto Najeriya daga durkushewa”
Da aka tambaye shi ko wane ne wannan mutumin da suke magana a kanshi, Shugabŕn Matasan Najeriyar yace Mutum ne sananne kuma haziki mara tsoro, ba Gwamna ba ne mai ci ko tsohon gwamna, shi jarumi ne kuma tsohon soja wanda kowa ya shaida gogewar shi, kuma nan bada jimawa ba za mu bayyana sunan shi ga ‘yan Nijeriya.
