Rahoton dake shigo mana yanzu haka daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun halaka Hassan Ahmed, Manjo Janar a Rudunar Sojojin Nigeria, a kan hanyar birnin tarayya Abuja.
An harbe Janar Ahmed, wanda a baya-bayan nan aka nada shi direkta a hedkwatar sojoji, a kusa da Abaji a babban birnin tarayya Abuja a daren ranar Alhamis.
Maharan, a cewar wani dan uwan marigayin sun kuma yi awon gaba da matarsa. Ahmed da matarsa suna dawowa daga Okene a jihar Kogi ne a lokacin da suka gamu da yan bindigan.
Rundunar Sojojin Nigeria ta tabbatar da rasuwar Manjo Janar Ahmed Kakakin rundunar sojoji, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya tabbatar da rasuwar Ahmed.
Ya ce babban hafsan sojojin kasa, Laftanat Janar Faruk Yahaya, ya aike da tawaga domin yi wa iyalan mammacin ta’aziyya.
